Connect with us

News

Jami’ar Northwest Ta Ƙara Kuɗin Makaranta Duk da Ragen Kashi 50% Da Gwamnatin Kano Ta Yi

Published

on

images (2)

Duk da ragin kuɗin makaranta da Gwamnatin Jihar Kano ta yi ga ɗaliban da suka fito daga jihar, Jami’ar Northwest da ke Kano ta sanar da sabon ƙarin kuɗin makaranta ga ɗalibanta

Sanarwar da Sashen Fasaha da Sadarwa (ICT) na jami’ar ya fitar ranar Lahadi, 1 ga Yuni, ta bayyana cewa sabon tsarin ya shafi dukkan ɗaliban da ke shirin dawowa makaranta, tare da shawartar su da su tabbatar sun ga sakamakon jarabawarsu kafin su biya kuɗin.

Advertisement

Jami’ar Northwest Ta Ƙara Kuɗin Makaranta Duk da Ragen Kashi 50% Da Gwamnatin Kano Ta Yi

A cikin sabon tsarin, ɗaliban da ke karantar BA. English za su biya fiye da ₦50,000, wanda ya fi yawancin sauran hanyoyin karatu tsada.

A baya, Gwamnatin Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rage kuɗin rajista da kashi 50 cikin 100 ga ɗaliban da suka fito daga jihar, don rage musu radadin tsadar rayuwa da ta biyo bayan cire tallafin man fetur.

Advertisement

Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na jihar ne ya sanar da hakan, yana mai cewa gwamnati ta fahimci yadda abubuwa suka ƙaru — daga kuɗin sufuri har zuwa kayan abinci da sauran muhimman abubuwa na rayuwa.

Sai dai da dama daga cikin ɗaliban Jami’ar Northwest sun bayyana rashin jin daɗinsu kan sabon ƙarin kuɗin makaranta, suna roƙon Gwamnan jihar da ya sa baki a lamarin.

Advertisement

 

INDEPENDENT MIRROR 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending