Connect with us

News

Wutar Lantarki Tayi Ajalin Mutum 5 A Gombe

Published

on

Duk da rashin wuta, kamfanin lantarki na Kaduna ya buƙaci a biya kuɗin wuta

Mutum biyar sun rasa rayukansu, yayin da wasu huɗu suka jikkata, sakamakon dawowar wata irin wutar lantarki mai ƙarfi a unguwar Tudun Wada Pantami da ke cikin birnin Gombe, babban birnin jihar Gombe.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da daren jiya, inda wutar lantarki da ta ɗauke a baya, ta dawo da ƙarfi fiye da kima, lamarin da ya haddasa tsinkewar igiyar wuta (high tension) da ta faɗo, tare da haddasa gobara da kuma shake mutane da wutar lantarki.

Advertisement

Bincike Ya Gano Cewa Musulunci Na Ƙara Karɓuwa A Duniya Fiye Da Kowanne Addini 

Wani mazaunin yankin mai suna Adamu Abubakar Kulani ya shaida wa Progress Radio cewa:“Da farko wutar ta dawo ba ƙarfi sosai, sai ta sake ɗaukawa. Amma daga baya da ta dawo sai kawai muka ga tartsatsi yana fitowa daga wayoyi. Sai ga high tension ya tsinke, kuma duk wanda ya kusanci ƙofa ko ƙarfe, wutar ta kama shi nan take.”

Lamarin ya tayar da tashin hankulan mazauna unguwar, inda wasu ke zargin cewa rashin ingancin aikin kamfanin rarraba wutar lantarki ne ya haddasa aukuwar hakan.

Advertisement

Wadanda suka jikkata an garzaya da su Babban Asibitin Gwamnati na Gombe, inda aka duba lafiyarsu, kafin daga bisani likitoci su sallame su bayan samun sauƙi.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin kamfanin rarraba wutar lantarki ba kan lamarin.

Advertisement

Wasu mazauna yankin sun nemi gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su binciki lamarin tare da ɗaukar matakin da ya dace, domin kauce wa faruwar irin wannan masifa a nan gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending