Connect with us

News

NECO Ta Shirya Jarabawar Shiga Makarantun Unity Colleges Ga Dalibai Sama Da 64,000

Published

on

Spread the love

Hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) ta gudanar da jarabawar shiga makarantun sakandaren gwamnati na tarayya, wato Unity Colleges, ga fiye da dalibai 64,000 daga Najeriya, Jamhuriyar Benin da Togo a ranar Asabar.

Wannan jarabawa, wacce aka fi sani da National Common Entrance Examination (NCEE), na bai wa ɗaliban firamare damar samun guraben karatu a makarantun gwamnatin tarayya da ke ko’ina cikin ƙasar nan.

Wutar Lantarki Tayi Ajalin Mutum 5 A Gombe

Ministar Ilimi ta ƙasa, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta halarci wasu cibiyoyin da ake gudanar da jarabawar a Abuja, ciki har da Model Secondary School, Maitama da Government Secondary School, Tudun Wada, inda ta bayyana gamsuwarta da yadda komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Advertisement

Farfesa Ahmad ta ce yawan ɗaliban da suka zauna jarabawar na nuna yadda iyaye da al’umma ke ƙara yarda da tsarin makarantu na gwamnatin tarayya.

“Daga cikin waɗanda suka zauna jarabawar, 34,000 mata ne yayin da 30,000 maza ne. Wannan ya nuna cewa yara mata na ƙara samun damar karatu a Najeriya,” in ji ta.

Shugaban NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi, ya ce Jihar Legas ce ta fi yawan ɗaliban da suka rubuta jarabawar da fiye da 15,000, yayin da Togo ta fi ƙaranci da ɗalibai 17.

Advertisement

Ya ƙara da cewa an samu ɗalibai 109 daga ƙasashen Jamhuriyar Benin da Togo, dukkaninsu ‘yan Najeriya ne da ke zaune a waɗannan ƙasashe.

Farfesa Wushishi ya bayyana cewa jarabawar ta gudana lafiya ba tare da wata matsala ba, kuma yara masu buƙatu na musamman sun samu kulawa ta musamman da kayan taimako da ma’aikata da suka dace.

A nata bangaren, Shugabar Sashen Ilimin Sakandare a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Binta Abdulkadir, ta ce tsarin karɓar ɗalibai zai kasance ne bisa cancanta, kaso-kaso na jihohi, da la’akari da yara masu buƙata ta musamman da kuma yaran ma’aikatan gwamnati.

Advertisement

Ta bayyana cewa za a fara tantancewa da karɓar ɗalibai bayan fitar da sakamakon jarabawar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ce ana gudanar da wannan jarabawa ne a duk shekara domin bai wa ɗaliban da suka kammala firamare damar shiga manyan makarantun gwamnati na tarayya da ke fadin ƙasar.

 

Advertisement

VANGUARD

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *