News
Farfesa Gwarzo Ya Samu Lambar Girmamawa A Faransa – Wakiliyar UNESCO Ta Halarta

Jami’ar Cité Universitaire de Paris, wacce ke daga cikin manyan jami’o’i a duniya, ta karrama Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da Lambar Girmamawa ta Musamman saboda gudunmawarsa wajen bunƙasa ilimi a Afirka da duniya baki ɗaya.
An mika lambar ne a yayin wani taron kasa da kasa da jami’ar ta shirya a ranar Juma’a, 13 ga Yuni, 2025, a matsayin wani bangare na bikin cika shekaru 100 da kafuwar jami’ar. Shugaban jami’ar, Sanata Jean Mac Sauve, shi ne ya mika lambar karramawar a gaban fitattun masana da shugabanni daga sassa daban-daban na duniya.
NECO Ta Shirya Jarabawar Shiga Makarantun Unity Colleges Ga Dalibai Sama Da 64,000
Sanata Sauve ya bayyana cewa Farfesa Gwarzo ya cancanci wannan karramawa saboda jajircewarsa da sadaukar da kansa wajen kafa cibiyoyin ilimi a Najeriya da sauran kasashen Afirka. Ya ce Farfesa Gwarzo ya nuna kima da kwazo matuƙa a fagen ilimi, musamman a matsayin ɗan tsohuwar makarantar Faransa.
Wakiliyar dindindin ta Najeriya a UNESCO, Jakadiya Dr. Hajo Sani, ita ce ta wakilci Najeriya a wajen bikin. Ta bayyana farin cikinta kan yadda jami’ar ta zaɓi Farfesa Gwarzo don wannan lambar yabo, tana mai cewa hakan shaida ce ta yadda Farfesan ke taka rawar gani wajen haɓaka harkar ilimi a matakin duniya.
> “Farfesa Gwarzo ya kafa jami’o’i guda uku a Najeriya kuma har ‘ya’yana biyu na daga cikin masu cin gajiyar ci gaban da ya samar. Wannan lamari ne mai girma kuma abin alfahari,” in ji Jakadiya Hajo.
A nasa bangaren, Farfesa Gwarzo ya bayyana godiyarsa ga jami’ar bisa wannan lambar yabo da ya ce za ta ƙara masa ƙarfin gwiwa wajen ci gaba da sadaukar da kai don ci gaban ilimi. Ya kuma yi kira ga matasa ‘yan Afirka da ke karatu a ƙasashen waje da su koma gida domin ba da gudunmawa wajen gina nahiyar da ke da buƙatar cigaba.
> “Wannan karramawa wata kwakkwarar shaida ce ta yadda ilimi ke da matuƙar muhimmanci wajen sauya rayuwar al’umma. Zan ci gaba da jagorantar jami’o’in MAAUN wajen samar da nagartaccen ilimi da ke da tasiri,” in ji shi.
Lambar girmamawar da aka ba Farfesa Gwarzo na daga cikin manyan lambobin yabo da jami’ar Cité Universitaire de Paris ke bayarwa ga fitattun mutane masu tasiri a duniya. Wannan ya kara ɗaga darajar Farfesa Gwarzo a idon duniya a matsayin gwarzon ilimi da wakili na gaskiya ga nahiyar Afirka.