News
Yadda Wani Matashi Ya Bankawa Kansa Wuta A Kano, Sabida Yana Son Zuwa Aljanna
Wani matashi mai suna Suleiman Muntari ya ƙone kansa da wuta a unguwar Diga da ke kan titin Panshekara a birnin Kano, da safiyar Litinin.
Shaidu sun ce matashin, wanda mazaunin Kofar Gadon Kaya ne, ya zuba fetur a jikinsa sannan ya kunna wuta da kansa, yana mai cewa yana so ya tafi Aljanna.
Gwamnati Ta Ayyana Laraba A Matsayin Ranar Hutu Ga Ma’aikata Bisa Ziyarar Tinubu
“Ya ce yana son zuwa Aljanna, kuma yana magana da yadda ba za ka ce yana cikin hankalinsa ba,” in ji Saminu Isah, wani mai gyaran taya da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.
Wata mazauniyar unguwar, Aisha Salisu, ta ce alamu sun nuna cewa Suleiman ba ya cikin hayyacinsa lokacin da ya aikata hakan.
“Za ka ji ƙamshin wani abu a jikinsa, yana kuma maganganun da ba a gane ba. Mutane sun firgita, wasu sun gudu, wasu kuma sun kokarta zuba masa ruwa,” in ji ta.
Wasu matasa sun jefar da shi cikin wani ramin ruwa da ke kusa da titi domin kashe wutar, amma ta riga ta yi mummunan barna.
“Fatar jikinsa har ta fara fita,” in ji wani direban babur, Ibrahim Jafar.
Hukumomi dai ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba har yanzu.
