News
Ba A Fadawa Tinubu Gaskiyar Halin Da Ƴan Najeriya Ke Ciki — Usman Bugaje
Ɗan gwagwarmayar siyasa kuma tsohon ɗan majalisa, Dr. Usman Bugaje, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai san hakikanin matsin da al’ummar Najeriya ke ciki ba, yana mai zargin cewa wasu daga cikin waɗanda ke kusa da shi suna ɓoye masa gaskiya.
Bugaje ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da Gidan Talabijin Na Channels, inda ya caccaki yadda gwamnati ke tafiyar da mulki, yana cewa kalaman da take furtawa ba su da nasaba da ainihin halin da talakawa ke fuskanta.
NUJ Ta Karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf A Bikin Cika Shekaru 70
“Abin da muke so mu gani shi ne matakai na ainihi — manufofi da tsarin shugabanci da zai inganta rayuwar jama’a,” in ji Bugaje.
Ya bayyana cewa hauhawar farashin kaya da ƙarancin damar samun abinci da magani sun ƙara tsananta wa al’umma rayuwa, yana mai cewa tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar ya gaza wajen kawo sauyi ga rayuwar ɗan ƙasa.
“Dimokuraɗiyya an kirkiro ta ne domin ta yi wa mutane aiki, amma shin tana yi musu aiki ne?” ya tambaya.
Bugaje ya ƙara da cewa yawaitar rashin tsaro, ƙarancin ayyukan yi, da rushewar ƙananan masana’antu na daga cikin abubuwan da ke nuna cewa tsarin mulkin bai ke tafiya yadda ya kamata ba.
A cewarsa, “Gwamnatin da ba za ta iya tabbatar da jin daɗin rayuwa da tsaron jama’a ba, ba ta da hurumin kiran kanta gwamnatin dimokuraɗiyya ta gaskiya.”
Sai dai duk da wannan suka, Bugaje ya jaddada cewa dimokuraɗiyya ita ce hanyar mulki mafi inganci, idan dai za a samu shugabanni nagari, masu gaskiya da tsoron Allah.
