Connect with us

News

Farfesa Gwarzo Ya Taya Tsohon Gwamnan Bauchi, Adamu Mu’azu, Murnar Cika Shekaru 70

Published

on

adamu muazu 750x536

Shugaban kuma wanda ya kafa MAAUN Group of Universities, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya taya tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu, murnar zagayowar cika shekaru 70 da haihuwa.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Farfesa Gwarzo ya bayyana Mu’azu a matsayin ɗan siyasa nagari da gogaggen jami’in gwamnati, wanda ya yi fice wajen jagorantar Jihar Bauchi da kuma bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban Najeriya.

Advertisement

‎Ba Wuta, Ba Oxygen” – Iyalin Marigayiya Amina Sun Danganta Mutuwarta da Sakacin Asibitin AKTH

“Ba tare da wata shakka ba, Alhaji Adamu Mu’azu ya kasance ɗaya daga cikin fitattun shugabannin da suka gudanar da mulki cikin kwarewa da hangen nesa, inda ya yi wa Jihar Bauchi gwamna na tsawon shekaru takwas,” in ji Gwarzo.

Ya ce, “A madadina da kuma madadin MAAUN Group of Universities, ina taya ka murna bisa wannan babbar rana. Muna addu’a ga Allah Madaukakin Sarki ya kara maka lafiya da tsawon rai.”

Advertisement

Farfesa Gwarzo ya kuma yi fatan Allah ya ba wa tsohon gwamnan ƙarfi da ƙoshin lafiya, domin ci gaba da bayar da gudunmawa ga ƙasa da al’ummar da ya yi wa hidima a tsawon shekaru.

“A wannan rana ta musamman, muna tare da dubban ’yan Najeriya wajen taya wannan jigo na siyasa da shugabanci murnar cika shekaru 70. Muna fatan Allah ya ƙara masa albarka da nasarori a rayuwa,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending