News
Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Ci Sanata Natasha Tarar Naira Miliyan 5 Kan Raina Kotu
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da laifin raina kotu, inda ta umarce ta da ta biya tarar Naira miliyan biyar tare da rubuta takardar neman afuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin ranar Juma’a, inda ta bayyana cewa Sanata Natasha ta karya umarnin kotu da ya haramta magana kan wata ƙara da ke gaban ta, ta hanyar wallafa wani abu da aka bayyana a matsayin barkwanci cikin neman afuwa a shafinta na Facebook ranar 7 ga Afrilu.
Hizba Ta Raba Aure Da Aka Ɗaura Ba Tare Da Izinin Iyayen Yara Ba A Kano
Kotu ta ce wannan matakin nata ya nuna rashin da’a da mutunta hukuncin da kotu ta bayar a baya, wanda ke tilasta wa bangarorin biyu da su dakatar da magana kan lamarin da ke gaban kotu.
A sakamakon haka, kotun ta umurci Sanata Natasha da ta rubuta cikakkiyar takardar neman afuwa, ta wallafa ta a jaridu biyu na ƙasa da kuma a shafinta na Facebook cikin kwanaki bakwai.
Baya ga hakan, kotun ta ci ta tarar Naira miliyan biyar a matsayin hukuncin raina kotu.
