Connect with us

News

ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Najeriya

Published

on

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, wato ASUU, ta tsunduma yajin aiki a duk faɗin Najeriya sakamakon rashin biyan albashin watan Yuni na shekarar 2025 ga mambobinta.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ne ya sanar da haka a wata takaitacciyar hira da manema labarai a birnin Abuja, ranar Litinin.

Advertisement

An Tsinci Gawar Ministan Da Putin Ya Kora

Ya ce yajin aikin ya biyo bayan shawarar da Majalisar Zartarwa ta ƙungiyar ASUU ta ƙasa (NEC) ta yanke, wadda ta umarci mambobinta da su dakatar da aiki idan gwamnati ta gaza biyan su albashi cikin kwana uku kamar yadda aka saba.

“Wannan mataki da muke ɗauka ba wani sabon yajin aiki ba ne, amma martani ne ga halin ƙuncin da malamanmu ke ciki. Ofishin Akanta-Janar na Ƙasa ne ke jinkirta biyan albashin da gangan,” in ji shi.

Advertisement

Ya ce wasu jami’o’in ƙasar kamar Jami’ar Jos da ta Abuja sun riga sun fara yajin aikin tun tuni.

Farfesa Piwuna ya bayyana cewa tun da aka sauya tsarin biyan albashi daga IPPIS zuwa GIFMIS, malaman jami’a ke fuskantar jinkiri wajen samun albashinsu, inda wasu ke shafe sama da sati kafin su samu biyan da ba ya isar su.

Advertisement

Baya ga albashin watan Yuni, ASUU na zargin gwamnati da rashin biyan haƙƙoƙin da suka haɗa da Earned Academic Allowances (EAA), inda ya ce har yanzu malaman jami’a na bin gwamnatin tarayya fiye da Naira biliyan 10 daga cikin biliyan 50 da aka amince a biya su.

Ya ce kungiyar ta yi ƙoƙari ta gana da hukumomin gwamnati domin bayyana matsalolin da suke fuskanta, amma babu wani matakin da aka ɗauka har zuwa yanzu.

Advertisement

Farfesa Piwuna ya ƙara da cewa duk wata jami’a da ba ta biya malamanta albashi ba, za ta ci gaba da kasancewa cikin yajin aiki har sai an warware matsalolin da ke akwai.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending