Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙayyade Shekarun Shiga Jami’a

Published

on

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana shekara 16 a matsayin mafi ƙarancin shekaru da ɗalibi zai iya fara karatu a jami’a.

Ministan Ilimi na Ƙasa, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin wani taron tattaunawa da aka shirya a Abuja kan manufofi da dokokin JAMB na shekarar 2025.

Advertisement

ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Najeriya

Alausa ya ce ƙudurin na daga cikin matakan tabbatar da daidaito tsakanin shekarun balaga da shirye-shiryen ɗalibi na jiki da tunani kafin ya shiga matakin karatun jami’a.

“Mun cimma matsaya kan cewa dole ne ɗalibi ya kai shekara 16 kafin a ba shi gurbin shiga jami’a. Wannan doka ce, kuma ba za mu canza ta ba,” in ji Ministan.

Advertisement

Ya bayyana cewa gwamnati ta lura da yadda wasu makarantu ke ƙoƙarin sauya shekarun haihuwar ɗalibai domin su samu gurbin karatu da wuri, yana mai gargaɗi cewa hakan ya sabawa doka kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

“Babu wani uzuri da zai sa makaranta ta canza shekarun ɗalibi. Wannan ƙeta doka ne kuma za a hukunta duk wanda ya yi haka,” in ji shi.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa matakan da za su inganta tsarin ilimi, musamman ta fuskar bin ƙa’idojin da suka dace da kimar jami’o’in ƙasa da ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending