News
Gwamnatin Katsina za ta bada fili mai girman hekta 50 domin aikin noma
Gwamnatin Jihar Katsina ta saka hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da hukumomi huɗu a kan bayar da fili mai girman hekta 50, domin shirin yin noma a dam ɗin Sabke.
Hukumomin sun haɗa da hukumar kula da asusun bunƙasa noma ta ƙasa, hukumar kula da cigaban tafkin Sokoto Rima,Morocco based department expert, da kuma OCP Africa.
KPP-CWC Ta Gano Magungunan Jabbu Da Darajarsu Ta Kai Sama Da Naira Biliyan 1.3 A Kano
Tawagar ta samu wakilcin shugaban kwamitin kula da ruwa na majalissar tarayya ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kaita/Jibia Hon. Sada Soli.
Da yake magana bayan da ya saka hannu akan yarjejeniyar Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana jin daɗin shi ganin yadda gwamnatin tarayya ta ɗauki jihar Katsina a matsayin inda za a fara yin gwajin shirin noman.
“Kawo wannan shiri ya nuna irin yadda shugaban ƙasa Asiwaju Bola Tinubu yake ƙaunar mutanen jihar Katsina”.
Gwamnan yace ganin cewa dam ɗin Sabke shine kaɗai wurin da aka ware domin yin gwajin wannan shiri, ya zama dole mu bayar da duk wani gudummuwar da ya kamata domin tabbatar wannan yarjejeniya.
“Ina da tabbacin cewa wannan hukumomi za su yi bakin ƙoƙarin su domin samun nasarar shirin, wanda muke da tabbacin da shekara mai zuwa bayan kammala noman damuna za’a dasa da na rani” cewar Gwamnan.
Yace gwamnatin sa shirye take domin ganin shirin ya samar da noma a kowane lokaci, rani da damuna, wanda yace hakan zai taimaka ma manoma samun abun yi a gaba ɗaya shekara.
Shima Hon. Sada Soli, ya bayyana irin yadda yake da tabbacin hukumomin da suke cikin shirin za su yi iya ƙoƙari domin ganin an samu nasara, “kuma ba zamu taɓa bari wannan shirin na gwaji ya samu matsala ba,”Soli yace.
Ɗan majalisar ya bayyana cewa idan shirin ya samu nasara, jihar Katsina na faɗaɗa irin wannan shiri a Dam ɗin Jibiya, Zobe, da Dallaje da ke jihar.
A nashi ɓangaren babban daraktan kula da noma na hukumar cigaban tafkin Sokoto Rima Alhaji Muttaqa Ahmed Badaru Jiƙamshi, yace Dam ɗin sabke wuri ne mai muhimmancin gaske wanda gwamnatin tarayya ta yi shi tun shekarar 2018.
Ya kuma bayyana an ɗauki tsawon lokaci ba tare da anyi amfani da kayan aikin wurin ba, amma wannan shiri na gwamnatin shugaban ƙasa Asiwaju Bola Tinubu na “Renewed Hope ” zai taimaka wajen farfaɗo da wurin.
Muttaqah Jiƙamshi ya kuma bayyana hukumar shi ta bayar da filin mai girman hekta 50, domin yin shirin wanda zai wadatar da abinci tare da samar da abun yi.
A nashi jawabin babban sakataren hukumar kula da asusun bunƙasa noma ta ƙasa Alhaji Muhammad Ibrahim, ya bayyana hukumar shi ta ziyarci jihar a kwanakin baya, inda gwamnan da kanshi ya raka su suka zagaya domin ganin halin da Dam ɗin na Sabke yake.
Wannan shiri zai taimaka ma ƙudurin Gwamna Raɗɗa na bunƙasa noma wanda yake cikin kundin mulkin shi na Gina Goben Mu “Building Your Future”.
BLUEPRINT
