Connect with us

News

KPP-CWC Ta Gano Magungunan Jabbu Da Darajarsu Ta Kai Sama Da Naira Biliyan 1.3 A Kano

Published

on

IMG 20250710 WA0013

An kama magungunan jabu da aka kiyasta darajarsu ta kai naira biliyan 1.3 a wani samame da aka gudanar a cikin Kano Economic City da ke Dangwaura, kan hanyar Zariya.

An kama magungunan ne ta hannun Cibiyar Rarraba Magunguna ta KPP-CWC (Kanawa Pharmaceutical Coordinated Wholesale Centre), a cewar Hajiya Furera Ado Muhammed, babbar jami’ar harhaɗa magunguna a cibiyar.

KPP-CWC Ta Gano Magungunan Jabbu Da Darajarsu Ta Kai Sama Da Naira Biliyan 1.3 A Kano

A lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis, Furera ta ce kamen ya biyo bayan sahihin bincike da kuma matakan da aka ɗauka tun bayan da aka rufe tsohuwar kasuwar magunguna da ba ta bin doka ba, aka kuma mayar da duk harkar sayar da magunguna zuwa wannan sabuwar cibiyar da gwamnati ta kafa.

Ta ce daga cikin samfuran da aka gwada domin gano sinadaran aiki (Active Ingredients Content – AIC), kusan kashi 40.3% sun gaza gwajin, lamarin da ke nuna cewa magungunan ba su da inganci.

“Wasu daga cikin magungunan sun hada da antimalaria, antibiotics da painkillers da ake amfani da su wajen jinyar yara, kuma irin waɗannan su ke haddasa gazawar jinya da asarar rayuka,” in ji ta.

Tuni aka mika magungunan da aka kama ga Kwamitin Jihar Kano kan Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi domin a lalata su.

Advertisement

Furera ta yabawa haɗin gwiwar hukumomin da ke sa ido a harkar magunguna, irinsu NAFDAC da Pharmacy Council of Nigeria (PCN), bisa goyon bayan da suka ba wa cibiyar KPP-CWC.

Ta kuma buƙaci jama’a da su guji siyan magunguna daga wuraren da ba su da rajista, tare da bin hanya ta doka wajen gudanar da sana’ar m

agani a jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending