News
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargaɗi Kan Yiwuwar Ambaliya A Kano Da Sauran Jihohi 10
Gwamnatin Tarayya ta fitar da gargaɗi kan yiwuwar ambaliya a Jihar Kano da wasu jihohi goma a faɗin ƙasar nan, daga ranar 16 zuwa 20 ga Yuli, 2025.
Wannan na cikin wata sanarwa da Cibiyar Fargabar Ambaliya ta Ƙasa (National Flood Early Warning Centre) ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta fitar ranar Laraba.
An Kama Dalibai 11 Da Ake Zargi Kan Kisan Dalibai Biyu A Makarantar Gwamnati A Kano
Jihohin da aka ambata a cikin rahoton sun haɗa da Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Borno, Cross River, Jigawa, Kano, Katsina, Plateau, Yobe da Zamfara.
A Kano, rahoton ya bayyana cewa ana sa ran za a samu ruwan sama mai yawa a yankunan Kunchi, Birnin Kano, Gezawa, Wudil, Bebeji, Sumaila da Tudun Wada – lamarin da ka iya janyo ambaliya da illa ga rayuka da dukiyoyi.
Daraktan Sashen Kula da Lalacewar Ƙasa, Ambaliya da Gabar Teku a Ma’aikatar Muhalli, Usman Abdullahi Bokani, ya ce hukumomin da abin ya shafa a jihohin da aka ambata su gaggauta ɗaukar matakan kariya.
Ya kuma bukaci al’umma da su kasance cikin shiri da kuma bin shawarwarin da hukumomi za su bayar domin rage haɗarin ambaliya.
