Connect with us

News

Yadda Tinubu Da ‘Yan Jam’iyyar Hadaka Ta ADC Suka Ki Kula Juna A Wurin Jana’izar Buhari

Published

on

1752709225049

A wurin taron jana’izar Buhari ranar Talata, yan siyasa da suka saba yin musabaha da juna musamman a tarukka irin haka, kowa ya kama gabansa a wurin taron jana’izar Buhari.

Jigajigan gwamnati har da shugaba Tinubu duk sun halarci jana’izar marigayi Buhari, sai dai kuma babu wanda ya kula wani, kowa gabansa kawai ya kama.

Advertisement

An Ciro Maciji Nau’in Kububuwa Daga Takalmin Mai Gadi

Tinubu wanda shi da kansa ya karbi gawar Buharia Katsina sannan aka rako gawar tare da shi har Daura, an yi komai a gabansa.

Haka kuma shima mataimakin shugaban kasan, ministoci, Yan Majalisun kasa, da gwamnoni duk sun halarci wannan taro, sai dai kuma an raba jiha yayin da wadanda suke jam’iyyar hadaka ta ADC da kuma wadanda ma ba su ga maciji da ‘yan APC duk suka rika wa juna hadarin kaji, na ciki na ciki, ba a ce wa kowa komai.

Advertisement

An yi Jana’izar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ranat Talata a garin Daura, kuma jana’izar ya samu halarta manyan yan siyasar Najeriya, sarakuna da attajiran kasan.

Jana’izar ta samu halartar manyan baki daga wajen ƙasa, ciki har da Firayim Ministan Jamhuriyar Nijar da tsohon shugaban ƙasar, wanda hakan ya nuna matsayin Buhari a idon duniya.

Advertisement

Marigayi Muhammadu Buhari ya rasu ne bayan dogon jinya, kuma an binne shi a garin Daura, inda aka gudanar da Sallar Jana’iza bisa tsarin Musulunci. Ya mulki Najeriya sau biyu — a matsayin shugaban mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, da kuma zababben shugaban ƙasa daga 2015 zuwa 2023.

Ya kasance ɗaya daga cikin ’yan siyasa da suka fi janyo hankalin talakawa a tarihin Najeriya, inda ya kafa tarihi ta hanyar yin takarar shugabancin ƙasa har sau huɗu kafin samun nasara a 2015.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending