Connect with us

News

Muna Sane Da Shirin Zanga-Zagar Da Tsoffin Jami’anmu Za Su Yi  —Rundunar Ƴan Sanda

Published

on

Police

Rundunar Ƴan Sanda ta Ƙasa ta bayyana cewa tana da cikakken masaniya kan shirin gudanar da zanga-zangar lumana da wasu tsoffin jami’anta da suka yi ritaya ke shirin yi domin neman hakkokinsu da kuma korafin rufe asusun bankunan ajiyarsu.

Mai magana da yawun rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce rundunar na bin diddigin duk wani ci gaba da ake samu kan batun, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da su guji siyasantar da lamarin.

Advertisement

Farfesa Gwarzo ya gwangwaje makarantar Intercontinental Schools da sabuwar mota mai kujera 30

“Rundunar ta samu sahihin labari dangane da shirin wasu tsoffin jami’anmu na gudanar da zanga-zanga, lamarin da ya jawo hankalin manyan jami’an tsaron ƙasa. Sai dai abin takaici shi ne yadda wasu ke ƙoƙarin mayar da wannan batu na jindadi da jinƙai zuwa wani lamari na siyasa,” in ji sanarwar.

Rundunar ta jaddada cewa batun da ake ta magana akai dangane da kamfanin da ke da alhakin biyan hakkokin ritaya ga tsoffin jami’an ’yan sanda ba sabo ba ne. A cewarta, tun shekarar 2024 ake ta tattauna wannan matsala, kuma ana ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin warware ta.

Advertisement

Sanarwar ta bayyana cewa babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Egbetokun, ya riga ya gana da masu ruwa da tsaki da nufin shawo kan matsalar ta hanyar doka da tsari, tare da samar da hanyoyin da za su tabbatar da adalci da daidaito.

“Rundunar ba ta hana kowa bayyana ra’ayinsa ba, musamman idan aka yi hakan cikin lumana da bin doka. Sai dai dole ne a tabbatar cewa ba a jefa ƙasa cikin rudani ko barazana ga zaman lafiya ba,” in ji Adejobi.

Advertisement

A ƙarshe, rundunar ta roƙi tsoffin jami’an da sauran jama’a da su ba gwamnati lokaci domin ci gaba da duba lamarin da nufin kawo maslaha mai ɗorewa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending