News
Hisba Za Ta Yiwa Tubabbun Yan Daba Auren Gata A Kano
Hukumar Hisba a jihar Kano ta ce za ta shirya wa tubabbun ’yan daba aure, a wani shiri da gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin mayar da matasa kan turbar rayuwa ta gari.
Babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana hakan bayan da matasa sama da dubu ɗaya suka aje makamai tare da yin nadama.
‘Sojoji Kaɗai Ba Za Su Iya Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga Ba’ – Uba Sani
A cewar sa, shirin na cikin wani tsari da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fito da shi don tallafawa matasa da suka tuba daga aikata laifi.
Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a shelkwatar ’yan sanda ta Bompai, Gwamna Abba Kabir Yusuf – wanda kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya ya wakilta – ya ce wannan tantancewar da rundunar ’yan sanda ta gudanar ita ce mataki na farko.
Ya ce daga baya hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA za ta sake tantance matasan, domin tabbatar da sahihancin tuban da suka yi.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnati za ta ba tubabbun matasan jari, ta koya musu sana’o’in dogaro da kai, tare da samar musu da guraben karatu ga masu sha’awar ci gaba da karatu.
Kwamishinan ’yan sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce aikin da aka ɗora musu na tantance matasan ya nuna irin jajircewar da gwamnatin Kano ta ke da shi wajen yaki da laifuka.
Babban kwamandan Hisba, Sheikh Daurawa, ya gargadi matasan da su tabbata sun yi tuban gaskiya, tare da shawarci sauran matasan da ba su aje makamai ba da su rungumi shirin domin suma su amfana.
Daga cikin jagororin matasan da suka yi magana akwai Kamilu da Buzu Mai Kidan Gangi, waɗanda suka gode wa gwamnati da kwamishinan yaɗa labarai da sauran shugabannin da suka tsaya domin ganin rayuwarsu ta inganta.
