News
‘Sojoji Kaɗai Ba Za Su Iya Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga Ba’ – Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana cewa yin amfani da sojoji da jami’an tsaro kaɗai ba zai kawo ƙarshen ta’addanci da ƙungiyoyin masu tayar da hankali a Arewa maso Yamma ba.
Ya ce matsalar tsaro a yankin ta samo asali ne daga talauci, rashin adalci, rashin damar matasa da kuma gazawar shugabanci.
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Muhimmancin Bin Ka’ida A Aikin Jarida
Gwamnan, wanda kwamishinan tsaron cikin gida Sule Shuaibu ya wakilta, ya yi wannan bayani a lokacin taron koli na yanki kan dabarun hana da kuma yaƙi da tsattsauran ra’ayi (PCVE) a Kaduna.
Ya ce tsattsauran ra’ayi na daga cikin manyan barazana ga ci gaban ƙasa, domin ya raba iyalai da gidajensu, ya lalata rayuwa da ilimi, ya kuma rusa amincewar jama’a da gwamnati.
Mai kula da Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Adamu Laka, ya yi kira ga a yi amfani da hanyoyin da al’umma za su jagoranta tare da dogaro da bayanan sirri wajen magance matsalar.
Ya bayyana cewa iyakokin da ba a tsare su ba, rikice-rikicen da sauyin yanayi ya jawo, da kuma raunin shugabanci sune ke ƙara rura wutar ta’addanci.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin PAVE, Jaiye Gaskiya, ya jaddada muhimmancin dawo da ikon kananan hukumomi, yana mai cewa shugabanci a matakin tushe shine ya fi kusanci da jama’a kuma ya fi sauƙin amsa bukatunsu.
Wannan ra’ayi ya yi daidai da yadda wasu shugabannin ‘yan bindiga kamar Bello Turji suka yi amfani da koke-koken Fulani wajen yaɗa tayar da hankali da ta’addanci.
A cikin shekarun baya, jihar Kaduna ta sha fama da hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a dazuzzuka, musamman a Kamuku da ya haɗa jihohin Zamfara da Neja.
Amma bayan sulhun da gwamnatin Kaduna ta shiga da wasu daga cikin ‘yan ta’addan, hare-hare sun ragu a wasu sassan.
Wannan ya nuna dalilin da ya sa Gwamna Sani ke cewa a haɗa dabarun soja da hanyoyin warware matsalolin zamantakewa kafin a iya samun dawwamammen zaman lafiya.
