News
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Muhimmancin Bin Ka’ida A Aikin Jarida
Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta ci gaba da yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da bin ƙa’ida da ɗabi’a a aikin jarida.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana haka ne lokacin da ƙungiyar Young Female Professionals in Media (YFPM) ta kai masa ziyara a ofishinsa.
Ya ce gwamnatin Kano ta damu da yadda ake yawaita bayanai marasa inganci a kafafen sada zumunta da ma kafafen gargajiya, lamarin da ya ce na iya lalata martabar jihar da kuma aikin jarida gaba ɗaya.
Kwamishinan ya kuma bayyana shirin gwamnati na haɗin gwiwa da ƙungiyar NUJ wajen kafa kwamiti na gogaggun ’yan jarida domin ƙarfafa bin ƙa’ida da inganta aikin jarida.
Tun da farko, Sakatariyar YFPM, Maryam Usman Nagado, ta ce ƙungiyar ta haɗu ne domin ƙarfafa mata a harkar jarida ta hanyar horo, wayar da kai da kuma samar da haɗin kai da hukumomi.
-
News21 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
