Connect with us

News

An Sace Dalibai 330, An Rufe Makarantu 52 A ƙananan hukumomi Uku A Katsina —Rahoto

Published

on

Bandits raze church two houses in Kaduna

Wani sabon rahoto da Cibiyar Oxford Policy Management (OPM) tare da goyon bayan UNICEF ta fitar ya nuna cewa tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025, an sace akalla dalibai 330 a ƙananan hukumomin Batsari, Faskari da Kankara na Jihar Katsina, lamarin da ya tilasta a rufe makarantu 52 a yankunan.

Rahoton wanda wata jami’a a cibiyar OPM, Hadiza Tijani, ta gabatar a taron wayar da kai da aka gudanar a Ranar Talata, ya bayyana cewa an kashe dalibai biyu da kuma malamai biyar, yayin da aka yi garkuwa da malamai 15.

Advertisement

Ya Kamata Ko Wanne Ɗan Nijeriya Ya Koyi Dabarun Kariyar Kai —Chris Musa 

Binciken ya ƙara da cewa kusan kashi 79.7% na ɗalibai na fuskantar matsalar rashin mai da hankali a darussa saboda tsoro da tashin hankali a makarantu. Haka kuma, malamai da dama sun bayyana cewa ba sa jin kansu cikin tsaro yayin gudanar da aikin koyarwa.

Rahoton ya yi nuni da cewa matsalar tsaro a yankunan karkara da kan iyaka na ci gaba da raunana sha’anin ilimi a Katsina.

Advertisement

Rahoto ya shawarci gwamnati da abokan hulɗa su ɗauki ƙarin matakan tsaro a makarantu, su kafa cibiyoyin koyarwa na wucin gadi, tare da tallafa wa malamai da ɗalibai da rikice-rikice suka shafa.

A nata jawabin, Kwamishinar Ilimi ta Jihar Katsina, Hajiya Zainab Musawa, ta ce duk da cewa hare-haren ‘yan bindiga sun ragu a wasu yankuna, akwai makarantu da dama da har yanzu ke ajiye ƙofa saboda tsoron sace dalibai.

Advertisement

 

DAILY NIGERIAN 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending