News
An Kone Motar ’Yan Sanda Bayan Rikicin Mutuwar Dan Acaba A Garko
Wani rikici da ya barke a karamar hukumar Garko, jihar Kano, ya yi sanadin konewar wata mota da ake zargin mallakin rundunar ’yan sanda ce a ofishinsu na yankin.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga fushin ’yan haya da babura (’yan acaba) da sauran jama’ar gari, bayan kama wasu mutane da ake zargin sun kashe wani dan acaba tare da kwace masa babur dinsa.
Babban Bankin Ghana (BoG) Ya Dakatar Da Lasisin Cinikin Kuɗaɗen Ƙetare Na UBA
Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Global Tracker cewa an cafke mutanen da ake zargi bayan bin sawun wayar da marigayin ya bari.
A cewarsa, “Ana zargin mutanen da suka tare wani matashi mai suna Umar Idris daga kauyen Kamfa, suka kwace masa babur sannan suka kashe shi a ranar Laraba da ta gabata, bayan ya dawo daga garin Buda.
An kama mutum biyu da ake zargi, ciki har da dan uwan marigayin. Sai dai abokan aikin Umar da sauran jama’ar gari suka dage sai an fito musu da wadanda ake zargi domin su kashe su, abin da ya janyo rikici tsakaninsu da ’yan sanda.”
Majiyar ta ce a cikin arangamar ne aka kona motar da ake zargin ta ’yan sanda ce, ko da yake ba a tabbatar da mallakinta ba.
Bayanan da Jaridar Inda Ranka ta tattara sun nuna cewa yanzu an samu natsuwa a yankin bayan da aka sake tura karin jami’an kwantar da tarzoma (MOPOL) domin tabbatar da doka da oda.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar na ci gaba da tattara bayanai a kan yadda lamarin ya faru.
