News
Jami’an ’Yansanda Sun Kama Mutum 158 Kan Laifuka Daban-daban A Jigawa
Rundunar ’Yansandan jihar Jigawa ta ce ta kama mutum 158 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin watanni biyu da suka gabata.
Kwamishinan ’Yan sandan jihar, CP Dahiru Muhammad, ya ce cikin waɗanda aka kama akwai mutum biyu da ake zargi da shugabancin ƙungiyar masu garkuwa da mutane.
Daga MAKAFI Zuwa AWAKAI: Baje-kolin Siyasar Tumasanci Da Bautar Gumakan Siyasa.
Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin su, Adamu Musa, mai shekara 47 daga unguwar Yalwawa a Dutse, ya amsa laifin yin garkuwa da mutane huɗu a Sumaila ta jihar Kano. An ce ya tsare su a kauyen Baranda na Dutse, inda daga baya ya sako su bayan ya karɓi kuɗin fansa da ya kai Naira miliyan takwas da babur mai darajar kusan Naira miliyan ɗaya.
A wani samame da aka yi a ranar 29 ga watan Agusta, jami’an ’yansanda tare da sa-kai sun kuma kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane da fashi da makami, Iro Garba, mai shekaru 25 daga Ajingi a Jihar Kano. Rundunar ta ce an kama shi da rigunan sojoji guda uku, kuma ya amsa cewa shi da wasu abokan harkallarsa sun yi garkuwa da mutane a Kano, Jigawa da Bauchi.
Haka nan kuma, ’yansanda sun ce sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da fasa shago a Malam Madori. An kwato akwati mai ɗauke da kuɗi Naira 870,000, wayoyi 20, na’urar PoS, da wasu kayayyaki daga hannunsu.
A cewar rundunar, cikin watanni biyu da suka gabata, mutanen da aka kama sun kai 156 bisa laifuka daban-daban kamar safarar makamai, fashi da makami, kisan kai, fyade, sata, da fataucin miyagun ƙwayoyi.
An kuma kwato makamai da dama, ciki har da bindigogi AK-47 guda biyu, motoci uku, adaidaita sahu ɗaya, shanu 14 da miyagun ƙwayoyi kamar tramadol, diazepam, exol da tabar wiwi.
Kwamishinan ya ce rundunar za ta ci gaba da kai farmaki kan masu aikata laifuka da masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar Jigawa.
