News
Yan Bindiga Sun Harbi Wani Saboda Rashin Isassun Kuɗi a Asusunsa A Delta
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta kama wasu mutum uku da ake zargi da karɓar Naira miliyan biyu daga hannun wani mutum, sannan suka harbe shi bayan sun gano ba shi da isassun kuɗi a asusun bankinsa.
Waɗanda ake zargin su ne Chukwuebuka Nka (25), Uche Okechukwu, da Somto Chukwuma. Sun harbi wanda abin ya shafa a ƙafarsa saboda rashin kuɗin da suke nema.
ALGION Ta Girmama Gwamna Abba Kabir Yusif Bisa Sauye-sauyen Da Ya Kawo A Fannin Yaɗa Labarai
Kakakin rundunar, DSP Bright Edafe, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa cewa an yi garkuwa da mutumin a gidansa da ke Ogwashi-Uku. ’Yan sanda sun bi sahun masu garkuwar har cikin daji, inda suka ceto wanda abin ya shafa da raunin harbin bindiga.
Bincike ya kai ga kama Nka da Okechukwu a Jihar Anambra, inda aka gano motar mutumin, ƙirar Toyota Venza, da aka yi amfani da ita wajen aikata laifin. Bayan haka, ’yan sanda sun kai samame wata mafakarsu a ƙauyen Agidiase, Ogwashi-Uku, inda aka kama Somto Chukwuma.
Rundunar ta kuma gano motar da masu garkuwar ke amfani da ita da na’urar katse sadarwa da kayan aikinsu. DSP Edafe ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da haɗin kai wajen tabbatar da tsaroa yankin.
