News
Har Yanzu Ba A San Inda Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Yake Ba
Rahotanni daga Jihar Kebbi sun tabbatar da cewa har yanzu ba a san inda Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Hon. Abubakar Bagudo, yake ba, bayan da wasu ‘yan bindiga suka sace shi a daren Juma’a.
Wani mazaunin yankin, Malam Abubakar Umar Bagudo, ya shaida wa Leadership cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne jim kadan bayan mataimakin kakakin ya idar da sallar Isha’i a masallacin da ke kusa da gidansa.
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Uku, Sun Yi Garkuwa Da Wasu A Kano
Ya ce, “Har safiyar jiya mun yi magana da shi a waya, inda ya roƙe ni da in sanar da iyalansa da abokansa su kwantar da hankalinsu, saboda ana ci gaba da tattaunawa tsakaninsa da ‘yan bindigar.”
Rahotanni sun kuma nuna cewa wani aboki nasa mai suna Abubakar na karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Birnin Kebbi, bayan da harbi ya same shi a lokacin harin.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Nafi’u Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tura jami’an Mopol da ke aiki tare da DPO na Bagudo domin bin sawun masu garkuwa da kuma tabbatar da cewa an kubutar da mataimakin kakakin cikin koshin lafiya.
A wani bayani da rundunar ‘yan sandan ta fitar daga baya, ta ce an kaddamar da babban samame tare da jami’an soji da na ‘yan sanda domin ceto wanda aka sace.
