Connect with us

News

Gwamnan Kano Ya Amince Da Manyan Ayyukan Inganta Asibitoci Da Samar Da Kayan Aiki Na Zamani A Kano

Published

on

IMG 20251104 WA0007

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da manyan ayyukan inganta asibitoci da samar da kayan aiki na zamani a wasu daga cikin cibiyoyin lafiya na jihar, karkashin shirin KHETFUND.

Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Dr. Mansur Mudi Nagoda, ya bayyana cewa amincewar gwamna ta shafi ayyuka da dama, ciki har da: samar da wutar lantarki ta hasken rana (solarization) a Asibitin Dambatta da Abubakar Imam Urology Center, sayen sabbin kayan aikin lafiya ga Asibitocin Tudun Wada da Doguwa, da kuma fadada sashen Gaggawa (A&E) na Asibitin Kwankwaso da gina bayan gida na VIP.

Advertisement

Kano: Matasa 1,654 Sun Ajiye Makamai, Ana Sa Ran Karin 2,100 Sakamakon Shirin Safe Corridor — Waiya

Dr. Nagoda ya ce manufar wannan shiri ita ce tabbatar da ingantaccen tsarin lafiya a jihar Kano ta hanyar sabbin gine-gine, kayan aiki na zamani, da inganta ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.

“Shirin samar da wutar lantarki daga hasken rana a asibitocin Dambatta da AIUC zai tabbatar da samun wutar da ba ta yankewa wajen gudanar da ayyukan likita na gaggawa, dakunan gwaje-gwaje, dakin tiyata, da sashen haihuwa. Wannan zai rage dogaro da wutar lantarki ta kasa, rage kudin gudanarwa, da kuma kare muhalli,” in ji Dr. Nagoda.

Advertisement

 

Haka kuma, sayen sabbin kayan aikin lafiya ga asibitocin Tudun Wada da Doguwa zai inganta gano cututtuka da saukaka ayyukan likitoci, yayin da fadada sashen Gaggawa da gina bayan gida na VIP a Asibitin Kwankwaso zai samar da yanayi mai jin dadi ga marasa lafiya, maziyarta, da ma’aikatan lafiya.

Advertisement

Dr. Nagoda ya jaddada cewa dukkan waɗannan ayyuka sun samu ne ta hanyar shirin KHETFUND karkashin jagorancin Sakatariyar Shirin, Dr. Fatima Zaharaddeen, wacce jajircewa da kirkirarta ke tabbatar da canji mai kyau a asibitocin jihar.

Sakataren ya gode kwarai ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon baya da jarin da yake zuba a fannin lafiya, inda ya bayyana cewa hakan na nuna kulawa, hangen nesa, da matukar son inganta rayuwar al’ummar Kano.

Advertisement

A karshe, Dr. Nagoda ya tabbatar da cewa hukumar za ta tabbatar da nasarar aiwatar da ayyukan tare da kiyaye su, cikin tsarin sauyi na kiwon lafiya da gwamnan ke jagoranta, domin samun Kano mai lafiya da ci gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending