Connect with us

News

Jami’an Tsaro Sun Kama Mutum Da Wayoyi 17 Na Sata A Wurin Sauya Shekar Gwamnan Bayelsa

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Jami’an tsaro a jihar Bayelsa sun kama wani mutum da ake zargi da sata, inda aka gano wayoyi 17 da kuma kudi a wurin taron sauya shekar Gwamna Douye Diri daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Taron, wanda ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni da manyan jami’an siyasa, ya gudana ne yayin da Gwamna Diri da yawancin ’yan majalisar dokokin jihar suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Advertisement

Gwamnan Kano Ya Amince Da Manyan Ayyukan Inganta Asibitoci Da Samar Da Kayan Aiki Na Zamani A Kano

Shugaban kungiyar sa-kai na jihar, Doubiye Alagba, wanda ya jagoranci kama wanda ake zargin, ya bayyana cewa an mika mutumin ga jami’an Operation Puff Adder na rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da cikakken bincike da gurfanar da shi a kotu.

 

Advertisement

A cewar Alagba, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya bayyana cewa ya shigo daga jihar Ribas ne domin yin amfani da taron siyasar wajen sata.

“Mun kama shi ne bayan mun lura da motsinsa da ya sa muka zarge shi. Da muka bincike jakarsa, sai muka gano wayoyi 17, kudi N91,000 da kuma katunan ATM da dama,” in ji Alagba.

Advertisement

Ya ce wanda ake zargin, mai suna Francis, ya bayyana cewa yana tare da wasu abokan laifi da suka tsere lokacin da jami’an tsaro suka iso wurin.

Alagba ya kara da cewa kafin a kama shi, tawagar masu satar sun riga sun kwashe sama da N400,000,

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending