News
Hukumar INEC ta bayyana damuwa kan rashin tsaro gabanin zaben Bayelsa,Kogi da Imo
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana damuwarta dangane da karuwar matsalar rashin tsaro da ake fama da ita, gabanin zaben gwamnoni da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Imo
A cikin wata sanarwa da kwamishinan hukumar na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Sam Olumekun ya fitar, ya bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu da su kaucewa ayyuka da kalaman da za su iya kawo matsala.
Majalissar Dattawa Ta Bukaci A Mika Matatun Man Fetur Ga Hannun Masu Zuba Jari
“Hukumar ta damu da yawaitar rashin tsaro da tashe-tashen hankula da suka hada da fada tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa da ‘yan takara a zabe mai zuwa,” inji shi.
Hukumar ta yi kira ga daukacin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su guji furta kalamai da abubuwan da ka iya zafafa al’amuran siyasa, inda ta kara da cewa za ta ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin tare da ci gaba da kulla huldar ta da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a jihohin uku
Wani labarin kuma Majalissar Dattawa Ta Bukaci A Mika Matatun Man Fetur Ga Hannun Masu Zuba Jari
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
