Connect with us

News

Ƴan Ta’adda Sun Sace Ɗalibai Da Dama, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makarantar A Kebbi 

Published

on

Spread the love

Wasu ƴan ta’adda ɗauke da miyagun makamai sun kai mummunan hari a wata makarantar ’yan mata da ke Jihar Kebbi da daren jiya, lamarin da ya jefa ɗalibai da mazauna yankin cikin firgici.

Maharan sun shiga makarantar ne suna harbe-harbe domin tsoratar da jama’a, sannan suka kutsa cikin ɗakunan kwana na ɗalibai.

‎Mace Ɗaya Ta Mutu, Shida Sun Jikkata Yayin Da Bus Ta Yi Karo Da Tipa 

A cewar majiyoyi, maharan sun yi awon gaba da ɗalibai da dama, bayan sun rinjayi jami’an tsaron makarantar. Da dama daga cikin ɗaliban da suka tsere sun fake a wasu ƙauyuka da ke kusa, yayin da ake ci gaba da gano adadin waɗanda aka sace.

Rahotanni sun tabbatar  da cewa, mataimakin shugaban makarantar Malam Hassan Yakubu Makuki ya rasa ransa yayin da yake ƙoƙarin kare ɗalibai daga maharan.

Advertisement

Jami’an tsaro sun isa yankin, kuma an ƙaddamar da bincike tare da farautar maharan domin ceto ɗaliban da aka sace.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi Allah-wadai da harin, tare da tabbatar wa jama’a cewa ana ɗaukar duk matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya.

 

 

Advertisement

GLOBAL TRACKER 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *