News
Ruftawar Mahakar Ma’adanai Ta Yi Ajalin Sama Da Mutum 100
Kimanin mutane sama da 100 sun halaka, sakamakon zaftarewar kasa a wajen hakar ma’adanan karkashin kasa ba bisa ka’ida ba a Jamhuriyar Dimukuradiyyar kwango, kamar yadda ‘yan sanda suka sanar ranar Lahadi.
Sanarwar ‘yan sandan ta ce ibtila’in ya faru ranar Juma’a a mahakar ma’adanai ta Mulondo Lwalaba, ta birnin Kolwezi na Lwalaba a kudancin kasar, wanda da farko aka yi hasashen cewa ma’aikata 70 kasar ta binne, to amma gawarwakin da aka zakulo zuwa safiyar Asabar sun kai 101, yayin da ake ci gaba da laluben sauran da ba gani ba.
Wani Matashi Ɗan Najeriya Ya Kashe Mahaifinsa, Ya Raunata ’Yan Uwansa Mata Biyu A Amurka
Ko a cikin watan Yunin 2025, makamancin hadarin ya janyo asarar rayukan masu hakar ma’adanai fiye da 200 a gabashin garin Rubaya na lardin arewacin Kivu.
