News
Kwastam Za Ta Fara Gwajin Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi Ga Sabbin Jami’ai Da Tsofaffi — CGC Adeniyi
Babban Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen fara gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ga sabbin jami’anta da ake shirin ɗauka, tare da tsoffin ma’aikata a fadin ƙasar.
Adeniyi ya sanar da hakan ne yayin taron shekara-shekara na CGC’s 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya ce daga ranar 21 ga Nuwamba, duk wani ɗan takara da ke neman aikin Kwastam dole ne ya bi ta gwajin gano amfani da ƙwayoyi kafin a ɗauke shi.
Shugaba Tinubu Ya Umarci jami’an Soji Su Mamaye Dazukan Kwara, Niger Da Kebbi Cikin Sa’o’i 24
A cewarsa, matakin ba zai tsaya ga sabbin ma’aikata ba, har da dukkan jami’an da ke aiki a yanzu, domin tabbatar da tsabtace hukumar daga duk wata alaƙa da miyagun ƙwayoyi.
“Ba wanda za mu tsallake. Dole kowane jami’i ya yi gwajin ƙwayoyi. Ba za mu ci gaba da kashe kuɗinmu wajen gyara halayyar ma’aikacin da ya lalace saboda amfani da ƙwayoyi ba,” in ji Adeniyi.
Ya bayyana cewa binciken hukumar ya gano cewa wasu daga cikin matsalolin da ake fuskanta daga manyan jami’ai na da nasaba da amfani da miyagun ƙwayoyi, lamarin da ya ce lokaci ya yi da za a yi tsauraran matakai.
CGC Adeniyi ya kuma ce hukumar ba za ta lamunci duk wani jami’i da ke aiki a cikin maye ba, domin hakan na iya jawo tsoma baki ga tsaro, bin doka da kuma aikin tattara haraji da aka dora musu.
Ya yi nuni da cewa wajibi ne jami’an Kwastam su kasance cikin koshin lafiya da ingantacciyar ƙwaƙwalwa domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A ƙarshe, ya shawarci ma’aikata su rika kula da lafiyarsu tare da yin gwaje-gwajen lafiya akai-akai saboda muhimmancin hakan ga aikin da suke yi.
