News
Shugaba Tinubu Ya Umarci jami’an Soji Su Mamaye Dazukan Kwara, Niger Da Kebbi Cikin Sa’o’i 24
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin ƙarin tsauraran matakan tsaro a manyan yankunan dazuka na jihohin Kwara, Niger da Kebbi sakamakon ƙarin tashin hankali na garkuwa da mutane da hare-haren ’yan ta’adda da aka samu a kwanakin baya.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa, a ƙarƙashin sabon umarnin, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) za ta fara gudanar da tsaron sama na awa 24 ba tare da yankewa ba a cikin zurfin dazukan waɗannan jihohi, inda hukumomin tsaro suka nuna cewa su ne manyan mafakar kungiyoyin ta’addanci da masu garkuwa da mutane.
Dan Fashi Ya Mutu A Hannun Jami’an Yansanda Bayan Ya Yi Yunkurin Tserewa Daga Ofishinsu
Ana sa ran hukumomin tsaro za su yi aiki tare domin binciko maboyar ’yan bindiga, hana motsin ƙungiyoyin ta’addanci a yankunan, tallafa wa sojojin ƙasa wajen kai farmaki da kuma kwato wuraren da aka mamaye.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da jama’a ke ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar sace-sace da hare-hare a Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma a kwanakin nan.
