News
Dan Fashi Ya Mutu A Hannun Jami’an Yansanda Bayan Ya Yi Yunkurin Tserewa Daga Ofishinsu
Rundunar ’yan sandan jihar Neja ta ce wani mutum da ake zargin ɗan fashi da makami ne, mai Suna Aliyu Salihu, ya mutu bayan harbin da jami’anta suka yi masa, lokacin da yake yunkurin tserewa daga ofishinsu na Maitumbi da ke Minna.
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 9:20 na safiyar Asabar, lokacin da Salihu ya nemi fita don yin bayan gida.
A cewar majiyar, daga nan sai ya kai wa jami’in da ke bakin aiki da kuma ɗaya daga cikin masu gadin ofishin duka, sannan ya tsallake katangar ofishin yana ƙoƙarin tserewa.
Daya daga cikin masu gadin ya bi shi, ya kuma yi harbi da nufin dakatar da shi, abin da ya jawo masa munanan raunuka. An garzaya da shi zuwa Asibitin ’Yan Sanda da ke Minna, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
An ajiye gawar a Asibitin Tarayya Minna domin ƙarin bincike.
Rundunar ’yan sandan ta ce za ta gudanar da binciken cikin gida kan yadda lamarin ya faru da ko an bi matakan aikin rundunar yadda ya kamata.
