Connect with us

News

Kuskure Ne Tattaunawa Da Ƴan Bindiga A Najeriya —Olusegun Obasanjo

Published

on

obasanjo 2

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi watsi da ra’ayin yin tattaunawa da ƴan bindiga ko ƴan ta’adda, yana mai cewa hakan ba hanya ce da za ta kawo ƙarshen matsalar tsaro ba.

Ya bayyana cewa halin da ake ciki yanzu yana nuna cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta da ƙarfin da ake buƙata wajen daƙile kashe-kashe da ta’addancin da ke yi wa ƙasa barazana.

Advertisement

Mutane 3 Sun Rasa Rayukansu A Wata Gobarar Tankar Man Fetur A Kano

Obasanjo, yayin taron bikin Kirsimeti na Unity Christmas Carol a jihar Filato, ya ce ba za a ci gaba da kallo ana kashe ƴan Nijeriya ba tare da hukumomi sun ɗauki matakin da ya dace ba. Ya bayyana cewa idan gwamnati ta kasa, ƴan ƙasa suna da ƴancin neman taimakon ƙasashen duniya domin kare rayukansu.

Ya tunatar da cewa tun kafin ya sauka daga mulki, Nijeriya ta riga ta mallaki fasahohin da za su iya gano duk wani mai laifi a duk inda yake ta hanyar tauraron ɗan adam da na’urorin gano motsi. A cewarsa, abin mamaki ne yadda fasahar da ake da ita ba a amfani da ita yadda ya kamata, sai ma a ci gaba da neman sulhu da mutane masu aikata miyagun laifuka.

Advertisement

Obasanjo ya jaddada cewa ba addu’a kaɗai za a yi ba, dole ne a matsa wa gwamnati da hukumomin tsaro su yi aikinsu yadda ya kamata. Ya ce kowanne rai da ya salwanta saboda ta’addanci babban abin kunya ne ga ƙasa, kuma dole ne a nemi haɗin gwuiwar ƙwararru, da jami’an tsaro da ma ƙasashen waje domin magance wannan matsala da ta daɗe tana addabar Nijeriya.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending