Connect with us

News

’Yan Bindiga Sun Hallaka Wata Mata, Sun Sace Mutane Uku A Kano

Published

on

IMG 4719 (1)

Rahotanni daga Jihar Kano na nuni da cewa wasu ’yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki kauyen Yankamaye da ke cikin Karamar Hukumar Tsanyawa, inda suka kashe wata mata tare da yin garkuwa da mutane uku.

Majiyoyi daga yankin sun shaida wa Daily Nigerian  cewa lamarin ya faru ne misalin 11 na dare a ranar Asabar, lokacin da mazauna garin ke shirin kwanciya.

Advertisement

‎Tarihin Takardun Kudi A Najeriya

Wani mazaunin kauyen ya ce maharan sun ajiye babur-baburansu a wajen garin sannan suka kutsa ta cikin duhu da ƙafa, domin kauce wa gano su.

A cewar majiyar, maharan sun kashe wata tsohuwa da harsashi bayan da ta roƙe su da su kyale ɗanta da suka ke ƙoƙarin tafi da shi.

Advertisement

“Sun harbe tsohuwar ne saboda ta nemi su bar mata ɗanta. Bayan sun kashe ta, sai suka tafi da shi,” in ji mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa saboda tsaro.

Bayan haka, ’yan bindigar sun shiga wani gida dabam inda suka yi garkuwa da mata biyu, ciki har da surukar kansila na yankin.

Advertisement

Rundunar ’yan sandan Kano ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa yanzu.

Kauyen Yankamaye, wanda ke da tazarar kusan kilomita biyar daga garin Rimaye na Jihar Katsina, na daga cikin yankunan da ke fuskantar hare-haren ’yan bindiga, musamman tun bayan da wasu kauyukan Katsina suka rattaba hannu kan yarjejeniyar “sulhu” da kungiyoyin da ke kai hare-hare.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending