News
Kotu Za Ta Daure Mahaifin Da Ya Kashe ‘Yarsa Saboda Barin Gashin Kanta Babu Lullubi
Masu gabatar da kara a ƙasar Holland na neman kotu ta yanke wa wani uba dan asalin Siriya, Khaled Al N., hukuncin ɗaurin shekaru 25, bisa zargin kashe ’yarsa, Ryan Al Najjar, mai shekaru 18, tare da jefar da gawarta cikin ruwa.
An gano gawar matashiyar ne a watan Mayu 2024, a bayan gari. Bayan gwajin forensik, aka gano DNA na mahaifinta a jikin gawar da kuma a kan sarkar wuyanta da abin kunnenta — lamarin da ya tabbatar da zargin da ake yi masa. Daga nan ne Khaled ya tsere zuwa Siriya, inda yake yanzu.
’Yan Bindiga Sun Hallaka Wata Mata, Sun Sace Mutane Uku A Kano
Haka kuma ana neman kotu ta yanke wa ’yan uwanta maza biyu da ake zargin sun taimaka wajen kisan, hukuncin shekaru 20 kowannensu.
Masu gabatar da kara sun ce Khaled ya aikata laifin ne saboda ’yarsa ta fara bin rayuwar kasashen yamma, ciki har da barin gashin kanta a bude da kin sanya hijabi, lamarin da ya haifar da sabani a cikin iyalin.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News13 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
