News
Jami’an ’Yan Sanda Sun Gano Zinaren Miliyan 23 Bayan Shekara 12 Da Ɓacewarsu A Borno
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno.
Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam.
Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida.
An Kama Mutum 4 Da Ake Zargin ’Yan Bindiga Ne Tashar Mota A Kano
Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu daraja da suka ɓace tun 2012, lokacin da ’yan Boko Haram suka ƙona gidaje da shaguna da yawa a cikin al’ummarmu.”
Ta jaddada cewa, “babu daga cikin zinare da aka samu ya ɓace ko ya lalace a lokacin mamayar Malam Fatori da ’yan ta’adda suka yi fiye da nawa.”
Wani babban jami’in Majalisar Ƙaramar Hukumar Abadam da ya sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya yaba wa ’yan sandan da aka tura don kare rayukan mutane da kadarorinsu a yankin Tafkin Chadi.
Bayan gano tsabar zinare na naira miliyan 23, jami’in ya lura cewa martanin ’yan sanda a ayyukan yaƙi da ta’addanci da ake ci gaba da yi wani abin karfafa gwiwa ne ga sojoji da sauran hukumomin tsaro a yankin Tafkin Chadi, wanda ya ƙunshi qananan hukumomi takwas da ke yankin.
