News
An Kama Mutum 4 Da Ake Zargin ’Yan Bindiga Ne Tashar Mota A Kano
An kama wasu mutum huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne ɗauke da makamai da ake zaton bindigogi ne a tashar mota ta Ƙofar Ruwa da ke Jihar Kano.
Tashar motar, wadda ke kusa da kasuwar kayan gini ta Ƙofar Ruwa a Ƙaramar Hukumar Dala.
Jami’an Yan Sanda Sun Haramta Goyo A Babura Masu Kafa 2 A Kano
A cewar mazauna yankin, an kama mutanen ne lokacin da suke ƙoƙarin shiga mota domin tafiya zuwa wani waje a cikin Kano.
“Mutanen da ke tashar motar ne suka lura da makaman da suke ɗauke da su. Take suka gaggauta sanar da jami’an tsaro, waɗanda suka kama su. Su huɗu ne gaba ɗaya,” in ji Musa Balarabe, wani mazaunin yankin.
Ya ce an kama su ne da misalin ƙarfe 1 na rana.
Da farko an kai su ofishin ’yan sanda na Ƙofar Ruwa, kafin daga bisani aka mayar da su ofishin Dala.
Wani mazaunin yankin, Umar Nuhu, ya ce yana cikin shagonsa da ke Kwanar Taya, kusa da ofishin ’yan sandan, lokacin da aka kawo mutanen.
Ya ce hakan ya jawo firgici, inda mutane suka fara gudu a ko’ina.
Nuhu, ya ƙara da cewa mutane da yawa sun yi dandazo a ofishin ’yan sandan, yayin da wasu matasan ke son ɗaukar doka a hannu.
Da aka tuntuɓi kakakin ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, bai ce komai kan lamarin ba.
Ya ce har yanzu suna tattara bayanai kafin su fitar da sanarwa.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
