News
Jami’an Yan Sanda Sun Haramta Goyo A Babura Masu Kafa 2 A Kano
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta sake jaddada haramcin daukar fasinja a kan dukkan babura, tare da takaita ayyukan babura masu hawa uku adaidita Sahu daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe a wasu kananan hukumomi na birnin Kano.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce matakin na nufin tabbatar da tsaro da kare lafiyar al’umma, da kuma hana yada bayanai marasa tushe da ke kawo rudani a cikin jama’a.
Haramcin ya shafi wadannan kananan hukumomi:
Kano Municipal, Gwale, Dala, Fagge, Nassarawa, Tarauni, Kumbotso, Ungogo (yankin Jido)Dawakin Kudu (Tambuwal, Gurjiya da Jido Ward)
Kwamishinan ya ce jami’an tsaro za su kama duk wanda aka samu yana karya wannan doka, sannan a gurfanar da shi a gaban shari’a. Ya kara da cewa direbobi da masu amfani da babura da adaidita Sahu su bi doka ba tare da jinkiri ba.
CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, jami’in hulda da jama’a na rundunar, ya ce rundunar tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Hanyoyi da Ababen Hawa ta Kano (KAROTA) za ta dauki duk matakan da suka dace don tabbatar da bin wannan doka domin tsaron dukkan mazauna jihar.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
