News
Yan Bindiga Sun Sace Mutane 25 A Wani Sabon Hari A Kano
Akalla mutane 25 ne ‘yan bindiga suka sace, yayin da wasu biyu suka jikkata, sakamakon sabon harin da aka kai a Unguwar Tsamiya ta Faruruwa da al’ummar Dabawa, karamar hukumar Shanono, jihar Kano.
Harin ya faru ne a daren Lahadi, kimanin awa 24 kacal bayan wani harin da aka kai a al’ummar Yan Kamaye, karamar hukumar Tsanyawa, inda mutane uku suka bace.
Yan bindiga sun farmaki al’ummomin ne da daddare, suna harbin bindigogi lokaci-lokaci, wanda ya haddasa fargaba kafin su sace mutane da dama.
Mai magana da yawun shugaban karamar hukumar Shanono, Ammar Wakili, ya tabbatar da harin amma ya ce hukumomi na ci gaba da tabbatar da cikakkun bayanai kafin a fitar da cikakker sanarwa.
“Lamarin ya faru, amma muna tabbatar da dukkan bayanai kafin mu fitar da sanarwa,” in ji Wakili.
Mazauna yankunan iyaka tsakanin Kano da Katsina sun bayyana damuwarsu kan tsananin fargaba, yayin da hare-haren ‘yan bindiga ke karuwa a cikin ‘yan watannin baya-bayan nan. Duk da matakan tsaro, mazauna na nuna tsoron cewa tashin hankali na kara yaduwa cikin garuruwan Kano.
