News
Kano: Duk Wanda Aka Kama Yana Achaba Za A Kwace Masa Babur Tare Da Daurin Watanni 6 Da Tara — Kwamishinan Shari’a
Gwamnatin Jihar Kano ta sake tunatar da jama’a cewa duk mai aikin ɗaukar fasinja da babur (Achaba) a wasu yankuna na birnin zai fuskanci hukuncin daurin watanni 6, tara N10,000 ko duk biyun, tare da kwace babur, idan aka kama yana karya doka.
Abdulkarim Kabiru Maude, SAN Babban Lauya Gwamnati, Kuma Kwamishinan Sharia Na Jihar Kano ne ya bayyana hakan ga manema labarai
”Ya ce dokar hana Achaba ta shafi Kananan Hukumomin: Kano Municipal, Gwale, Dala, Nassarawa, Tarauni, Ungogo, Dawakin Kudu, Fagge, da Kumbotso.”
Ga sauran Kananan Hukumomin da aka amince da Achaba, gwamnati ta ce masu sana’ar dole su yi rajista da Mai Unguwa, Sashen Ayyuka na Karamar Hukuma da Ofishin ‘Yan Sanda domin inganta tsaro a harkar sufuri.
Kwamishinan Shari’a, ya ce gwamnati za ta ci gaba da tsaurara matakai domin tabbatar da tsaro da doka, tare da kira ga shugabannin al’umma da masu sana’ar Achaba da su yi biyayya ga doka.
-
News7 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
