Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Wani Matashi Hukuncin Kisa A Kano

Published

on

kotu

Wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai shekaru 22, Najibullah Alkasim, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe maƙwabcinsa, Isyaku Ya’u, a lokacin wata takaddama a shekarar 2024.

Alkaliya Farida Dabappa, wacce ta yanke hukuncin A ranar Litinin, ta yanke hukuncin cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin kisan kai ga wanda ake tuhuma ba tare da wata shakka ba.

Advertisement

Da Dumi- Dumi : Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Ajiye Muƙaminsa.

 

Ta yanke hukuncin cewa, Alkasim ne ya yi sanadiyyar mutuwar wanda aka kashe da gangan ta hanyar daɓa masa sukundireba a ƙirji.

Advertisement

“Na yanke wa Alkasim hukuncin kisa ta hanyar ratayewa saboda daɓa wa mamacin sukundireba da ta yi sanadin mutuwarsa,” in ji Alkaliya.

Lauyan masu gabatar da kara, Lamido Abba-Sorondinki, ya shaida wa kotun cewa, lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Janairu, 2024, a garin Dawakin Dakata, Kano.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending