Connect with us

News

‎Soyinka Ya Caccaki Shugaba Tinubu Kan Tura Sojoji Benin, Ya Ce Iya Sojojin Da Ke Tsaron Ɗansa Sun Isa Su Samar Da Tsaro ‎

Published

on

Farfesa Wole Soyinka

Fitaccen marubucin nan kuma mai lambar yabo ta Nobel, Farfa Wole Soyinka, ya soki matakin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na tura dakarun Sojojin Sama zuwa Jamhuriyar Benin bayan yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba.

‎Soyinka ya bayyana haka ne a yayin bikin shekara-shekara na bayar da kyaututtuka da Cibiyar Bincike ta Wole Soyinka (WSCIJ) ta shirya a Legas.

Advertisement

Gwamnati Za Ta Ci Tarar Naira miliyan biyu Ga Duk Wanda Ya Zubar Da Shara Ba Bisa Ka’ida Ba

‎A cewarsa, matakin tura sojoji ya yi nauyi fiye da kima, ganin cewa ma sojojin da ke gadin ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, sun isa su kare ƙasar Benin.

‎Ya ce“Shugaba Tinubu bai kamata ya tura sojoji ba domin shawo kan wannan tashin hankali. Rundunar da za ta iya yin wannan aiki tana nan a Legas ko Abuja, ba sai an tura manyan sojojin sama da na ƙasa ba.”

Advertisement

‎Soyinka ya ba da misalin yadda ya ga tarin jami’an tsaro a Legas lokacin da Seyi Tinubu ya isa wani otel a Ikoyi.

‎ “Na ga akalla jami’an tsaro 15 dauke da manyan makamai suna gadin Seyi Tinubu. Wannan ma ya wadatar da za a kare makwabciya kamar Benin.”

Advertisement

‎Ya ce yawan jami’an tsaron da ake zagaye ɗan shugaban ƙasa da su ya kai har ya fara tunanin tattaunawa da mashawaracin shugaban ƙasa kan tsaro.

‎Soyinka ya kuma ce ba Tinubu ne shugaban da ya fara mulki yana da ’ya’ya ba, amma bai ga dalilin da zai sa a girke tarin jami’an tsaro domin gadin ɗansa ba.

Advertisement

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending