News
’Yan Najeriya 32 Aka Kora Daga Indiya Kan Tuhumar Safarar Miyagun Ƙwayoyi
‘Yan Najeriya 32 aka kora daga Indiya bayan tuhumarsu da hannu a harkar safarar miyagun ƙwayoyi, a wani babban bincike da ‘yan sanda suka gudanar.
A ƙarshen watan da ya gabata, ‘yan Najeriya 50 ne aka kama a babban aikin cafke masu safarar miyagun ƙwayoyi a babban birnin Delhi, inda ‘yan sanda na Delhi suka yi aiki tare da rundunar EAGLE ta jihar Telangana.
China Ta Aiwatar Da Hukuncin Kisa Kan Wani Tsohon Ma’aikacin Banki Kan Karɓar Cin Hanci
Bincike ya nuna cewa waɗanda ake tuhuma suna da alaƙa da wata babbar ƙungiya ta safarar miyagun ƙwayoyi da harkar bakakin kuɗi (“hawala”) wadda ke yaduwa a manyan birane da dama a Indiya.
Masu laifin sun rarraba ƙwayoyi ta amfani da sabis na aika kaya, suna ɓoye su a cikin kayayyakin da ake tuƙa wa mutane.
An gano cewa masu safarar suna aiki ne ƙarƙashin wani mutum mai suna Nick, wanda ake zargin yana gudanar da harkokinsa daga Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa Nick na da akalla abokan hulɗa 100 a Delhi, sannan yana da abokan hulɗa sama da 3,000 a fadin Indiya.
Daga cikin mutanen da aka kama, ‘yan Najeriya 32 ne aka kora cikin gaggawa, yayin da aka buɗe shari’a kan wasu mutum bakwai da aka samu da ƙwayoyi a hannunsu.
Ana ci gaba da bincike, kuma ana sa ran nan ba da jimawa ba za a gano sauran mutane ko kamfanoni da suka taimaka wa waɗannan ƙungiyoyi wajen Safarar bakakin kuɗaɗe.
