Connect with us

News

Jihar Ebonyi: Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda Ya Rasu Yayin Taron Gudanarwa

Published

on

Rundunar ’yan sandan Jihar Ebonyi ta tabbatar da rasuwar wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda (ACP), Ogbon-inu Popoola, wanda ya rasu yayin da yake halartar taron shugabanci na rundunar.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Joshua Ukandu, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba a Abakaliki, babban birnin jihar.

Advertisement

Kotu Ta Sake Haramta Wa Ƴan Sanda Tilasta Bin Dokar Amfani Da Gilashi Mai Duhu

A cewarsa, marigayin ya fara fama da matsalar numfashi ne kwatsam a lokacin taron, lamarin da ya sa aka garzaya da shi zuwa asibitin rundunar da ke hedkwatar ’yan sanda, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Kafin rasuwarsa, ACP Ogbon-inu Popoola shi ne ke kula da Sashen Leken Asiri na Jihar (State Intelligence Department – SID).

Advertisement

Rundunar ta bayyana marigayin a matsayin jami’i mai jajircewa da kwarewa, wanda ya yi wa ƙasar hidima cikin gaskiya .

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending