News
Dangote Ya Yi Barazanar Shigar Da Ƙarar Bisa Zargin Batanci Tare Da Neman Diyyar Bilyan 100 kan Ɗan Kasuwa A Kaduna.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Group, Aliko Dangote, ya bai wa wani ɗan kasuwa da ke jihar Kaduna, Kailani Mohammed, wa’adin kwanaki 7 domin ya janye wata wallafa da ake zargin ta ɓata suna tare da neman afuwa a bainar jama’a.
Dangote ya bayyana cewa idan har Engr. Kailani Mohammed bai janye kalaman da ya yi ba, kuma bai gyara zargin da ya shafi shi da harkokin kasuwancinsa ba, to ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen shigar da ƙarar batanci (libel) a kotu, inda zai nemi diya ta naira biliyan 100 (₦100bn).
An Ceto Ragowar Daliban Makarantar Papiri 130 Dake Hannun ‘Yan Bindiga
A cewar sanarwar da aka fitar daga lauyoyin Dangote, zargin da aka wallafa ba shi da tushe, kuma yana da illa ga mutunci da martabar sa da kuma sunan kamfanoninsa a idon jama’a da kasuwanci.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Engr. Kailani Mohammed bai fitar da wata sanarwa ko martani a hukumance ba dangane da wannan wa’adi.
