Connect with us

News

An Cafke Wata Mata Bisa Zargin Shirya Sace Kanta Tare Da Karɓar Kuɗin Fansa Daga Hannun Mijinta.

Published

on

images 32

Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Lagos ta kama wata matar aure ’yar shekara 26 tare da wani abokinta mai shekaru 30 bisa zargin shirya sace kanta tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 2.5 daga mijinta.

Kakakin rundunar, Abimbola Adebisi, ta tabbatar da kamen a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar a Lagos.

‎ ‎Ofishin Jakadancin Amurka Ya Sanar Da Dakatar Da Bayar Da ‘Visa’ Ga ‘Yan Najeriya ‎

A cewar Adebisi, rundunar ta samu kiran gaggawa a ranar 24 ga Nuwamba daga hannun mijin wadda ake zargi ta ɗaya daga cikin layukan gaggawa, yana cewa an sace matarsa.

Ta ce mai kiran ya bayyana cewa waɗanda ake zargin masu garkuwa sun fara neman kuɗin fansa Naira miliyan 10, daga bisani suka rage zuwa Naira miliyan 3, amma duk da biyan Naira miliyan 2.5, ba a sako matar ba.

A yayin tambayoyi, Adebisi ta ce matar ta yi iƙirarin cewa mutane shida masu makamai ne suka sace ta a cikin wata mota Toyota Venza mai launin azurfa, suka kai ta maboyarsu tare da kwace mata wayarta iPhone 12 Pro Max.

“Ta kuma ce kuɗin fansar da mijinta ya biya an fara tura su zuwa asusun bankinta kafin a miƙa wa masu garkuwa da mutanen,” in ji ta.

Advertisement

Sai dai kakakin ta ce binciken ’yan sanda ya gano rashin daidaito da dama a cikin bayananta.

Ta ce a ranar 3 ga Disamba, jami’ai sun kama abokin hadin laifin a yankin Ede na Jihar Osun, inda aka kwato katin SIM da aka yi amfani da shi wajen rijistar asusun WhatsApp da aka gudanar da tattaunawar fansa ta hanyar sa.

“Yayin tambayoyi, abokin aikata laifin ya amsa cewa wadda ake zargi ce ta nemi amfani da layinsa domin ƙirƙirar asusun WhatsApp da aka yi amfani da shi wajen biyan kudin fansa.

“Ya kuma amince da ba ta lambar sirri ta wucin gadi (OTP) da aka turo wa layinsa, wanda hakan ya ba ta damar sarrafa asusun,” Adebisi ta bayyana.

Adebisi ta ƙara da cewa ƙarin bincike ya kai ga gano wayar iPhone 12 Pro Max ɗin da matar ta yi ikirarin tana hannun masu garkuwa.

“An kwato wayar daga hannun wani mutum mai shekaru 34, wanda ya shaida wa masu bincike cewa ya saye ta daga wadda ake zargi kan Naira 380,000, bayan an gargaɗe shi kada ya saka kowane katin SIM a cikin wayar,” in ji ta.

Advertisement

Ta ce bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da wadda ake zargi da abokin hadin laifinta a gaban kotu bayan kammala binciken.

 

PREMIUM TIMES

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending