News
Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai Ya Mika Ta’aziya Bisa Rasuwar Majalisar Dokokin Kano Biyu
Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Alhaji Adamu Ali Kibiya, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar mambobin majalisar dokokin jihar Kano su biyu da Allah Ya yi wa rasuwa da yammacin Laraba.
A cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Alhamis, Kwamishinan ya ce rasuwar ’yan majalisar ta kasance babban rashi, ba ga iyalansu da mazaɓunsu kaɗai ba, har ma da Jihar Kano da ƙasar nan baki ɗaya.
‘Yan Najeriya sun biya ‘yan bindiga N2.57bn a matsayin kudin fansa a shekara daya – Rahoto
Kibiya ya bayyana rasuwar wadannan mambobin majalisar biyu Sarki Aliyu Daneji, wakilin karamar hukumar birnin Kano wanda ya rike shugabancin Kwamitin aikin Hajji da Aminu Sa’adu dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ungoggo wanda ya rike Kwamitin kasafi a matsayin rashin da ya kada al’ummar jihar da kuma ba za a manta ba a tarihin jihar.
Kibiya yace rashin ‘yanmajalisar dokokin jihar su biyu sa’oi kadan tsakaninsu abin tashin hankali ne wanda kuma ya girgiza gwamnatin Kano da al’ummar jihar.
Yace ‘yanmajalisa ne abin dogaro ga al’umma da suka yi aiki tukuru wajen hidimtawa al’ummarsu tun daga tushe wadanda kuma maye gurbinsu zai zamo abu mai wahala.
Kibiya ya mika sakon taaziyarsa ga iyalan mamatan da mambobin majalisar dokokin jihar Kano da kafatanin al’ummar jihar Kano baki daya.
Ya kuma yi addu’a Allah Ya jikansu Ya sa Aljamnah Firdausi ta zamo makoma a gare su.
