News
‘Yan Najeriya sun biya ‘yan bindiga N2.57bn a matsayin kudin fansa a shekara daya – Rahoto
Wani sabon rahoto da cibiyar bincike ta SBM Intelligence ta fitar ya nuna cewa ’yan bindiga sun karɓi aƙalla Naira biliyan 2.57 a matsayin kuɗin fansa daga hannun mutanen da suka yi garkuwa da su a Najeriya, tsakanin Yuli 2024 zuwa Yuni 2025.
Rahoton, wanda aka fitar a ranar 19 ga Disamba, 2025, ya yi nazari kan manyan abubuwan tattalin arziki da siyasa da ke tasiri a nahiyar Afirka a shekarar 2025, tare da mai da hankali kan matsalar tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a Najeriya.
Dan Majalisar Jiha Na Karamar Hukumar Birni Sarki Aliyu Daneji Ya Rasu
SBM Intelligence ta bayyana cewa a cikin wannan wa’adin na shekara guda, ’yan bindiga sun nemi aƙalla Naira biliyan 48 a matsayin kuɗin fansa daga waɗanda suka yi garkuwa da su da iyalansu. Sai dai rahoton ya nuna cewa ƙananan kaso ne kawai daga cikin wannan adadi aka samu aka biya, duk da haka har yanzu kuɗin da aka karɓa ya kai biliyoyin naira.
Masana tsaro sun jaddada cewa ci gaba da biyan kuɗin fansa na ƙara ƙarfafa harkar garkuwa da mutane, tare da zama babbar barazana ga tsaron al’umma da tattalin arzikin ƙasa. Rahoton ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara matakan daƙile ayyukan ’yan bindiga, tare da kare fararen hula daga wannan masifa.
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News7 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
