Connect with us

News

Anthony Joshsua Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Hatsarin Mota

Published

on

1767027851599
Spread the love

Shahararren dan damben boksin na duniya, Anthony Joshua, ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota a ranar Litinin.

Mutum biyu sun rasu a bayan motar da Anthony Joshua yake ciki ta yi gaba-da-gaba da wata babbar mota da ke ajiye a gefen titin, a yankin Makun da ke Jihar Ogun.

Siyasar Kano: Shin Kwankwaso Ne Zai Tura Gwamna Abba Jam’iyyar APC ko Kuwa Gaban Kansa Yake Son Yi?

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa hatsarin ya auku ne a kan babban titin Legas zuwa Ibadan, inda motar da yake ciki ta yi kaca-kaca.

kakakin Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) na Jihar Ogun, Afolabi Odunsi ya tabbatar da hatsarin da kuma mutuwar mutanen ga wakilinmu.

Advertisement

Ya ce, “Gaskiya ne, (Joshua) yana nan da ransa. Mutum biyar ne hatsarin ya rutsa da su, amma biyu su mutu. Zuwa anjima za mu fitar da sanarwa.”

Anthony Joshua wanda ke zaune a kasar Birtaniya dan asalin yankin Shagamu ne a Karamar Hukumar Shagamu ta Jihar Ogun

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *