Connect with us

News

Najeriya Ta Kama Hanyar Zama Ƙasa Mai Jam’iyya Ɗaya Tal – Masana

Published

on

Tinubu
Spread the love

A wani yanayi da ƴan siyasa ke ci gaba da sauya sheƙa daga jam’iyyunsu zuwa jam’iyya mai mulki saboda fargabar kufcewar kujerar da suke kai, masana a ɓangaren na siyasa na gargaɗi kan yiwuwar rikiɗewar Najeriya zuwa ƙasa mai amfani da jam’iyya tal, wanda zai iya illa ga yiwuwar ɗorewar demokrɗiyya.

A cewar masana a fagen na siyasa da Demokraɗiyya siyasar ƙasa akan jam’iyya ɗaya ba tare da samun ɓangaren adawa mai ƙarfi ba shi ke nuna gazawar siyasa ko rashin bayar da dama ga ɓangarori wanda kai tsaye zai naƙasu ga ɗorewar demokraɗiyya.

‎KANO: Rayuwar Manoma Na Fuskantar Barazana Saboda Hakar Yashi A Madobi ‎

Kawo yanzu jam’iyya mai mulki ta APC ta mamaye jihohi 30 daga cikin 36 da Najeriya ke da su, bayan ficewar gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang daga PDP zuwa APC a baya-bayan nan yayinda ake jita-jitar sauya sheƙar Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC.

Bayan komawar Mutfwang APC a jiya, a jumalace APC na da jihohi 28 wanda shi ne mafi ƙololuwa da PDP ta taɓa haɗawa bayan babban zaɓen 2003 gabanin fuskantar tarnaƙi.

Advertisement

A gefe guda akwai Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da ke jam’iyyar PDP da Alex Otti na Abia da ke jam’iyyar Labour da dukkaninsu APC ke zawarci yanzu haka.

Sai dai duk da yadda jam’iyyun da ke mulki a kowanne matakai kan ji daɗi da zarar an samu ɓallowar magoya baya daga wata jam’iyya zuwa wata, masanan na kallon matakin a matsayin wani lamari da ke kassara siyasar ƙasa.

Masanan sun alaƙanta rashin aƙida ta siyasa a matsayin manyan dalilan da ke haddasa sauya sheƙar a tsakanin ƴan siyasa walau masu riƙe da madafun iko ko akasin haka.

 

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *