News
Dakarun Soji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Shirya Harin Bam A Masallacin Maiduguri
Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas ƙarƙashin Operation HADIN KAI sun sanar da kama wani mutum da ake zargi da jagorantar shirya harin kunar baƙin wake da ya kashe mutane biyar tare da jikkata wasu da dama a wani masallaci da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Kakakin rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri, inda ya bayyana sunansa da Sheriff Umra, wanda ya ce ta ka muhimmiyar rawa wajen tsara hare-haren kunar baƙin wake a yankin Arewa maso Gabas.
Najeriya Ta Kama Hanyar Zama Ƙasa Mai Jam’iyya Ɗaya Tal – Masana
A cewar sanarwar, jami’an tsaro sun kai samame a unguwar Kalmari ta Maiduguri a ranar 31 ga Disamba, 2025, wanda ya kai ga kama mutane 14 da ake zargi da alaƙa da ayyukan ta’addanci.
Rundunar ta ce bincike ya nuna Sheriff Umra—wanda ake kira da “Yusuf”—shi ne ke ɗaukar mutane, shirya su, da tura su domin kai hare-haren kunar baƙin wake, tare da samar da kayan haɗa bam.
Sojojin sun danganta shi da harin da aka kai Masallacin Kasuwar Gamboru a ranar 24 ga Disamba, inda wani dan kunar baƙin wake mai suna Adamu ya tayar da bam ya kuma rasa ransa.
Har ila yau, an ce yana da hannu a wani yunƙurin harin kunar baƙin wake da ya ci tura a Damaturu, inda ake zargin shi ne ya samar da sassan bam.
Binciken ya kuma nuna yiwuwar shigar wasu ‘yan uwansa cikin lamarin, ciki har da matarsa, Yagana Modu, yayin da ‘yarsa ta gida ta tabbatar da ganin wani da ake zargin dan kunar baƙin wake a cikin gidansu.
Rundunar ta ce dukkan waɗanda aka kama suna tsare, ana ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu da kuma tarwatsa cibiyar ta’addancin gaba ɗaya.
